Abdulsalami Abubakar
Abdulsalami Abubakar, shi tsohon janar ɗin Soja ne kuma ɗan Siyasa a Najeriya da yayi mulki na ɗan lokaci sannan ya miƙawa farar hula a tsakanin shekara ta alif ɗari tara da casa'in da takwas (1998 A.c) zuwa shekarar alif ɗari tara da casa'in da tara (1999).[1] An haife shi a shekara ta alif ɗari tara da arba'in da biyu 1942 a birnin Minna, Jihar Neja dake arewacin Najeriya (a yau jihar Neja). Abdulsalami Abubakar yazama shugaban ƙasar Najeriya bayan rasuwar Janar Sani Abacha, yayi mulki daga watan Yunin shekara ta alif ɗari tara da chasa'in da takwas 1998 zuwa watan Mayun shekarar alif ɗari tara da chasa'in da tara 1999 (bayan Sani Abacha - kafin Olusegun Obasanjo).
Abdulsalami Abubakar | |||||
---|---|---|---|---|---|
8 ga Yuni, 1998 - 29 Mayu 1999 ← Sani Abacha - Olusegun Obasanjo →
21 Disamba 1997 - 9 ga Yuni, 1998 | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Minna, 13 ga Yuni, 1942 (82 shekaru) | ||||
ƙasa |
Colony and Protectorate of Nigeria (en) Taraiyar Najeriya Jamhuriyar Najeriya ta farko Jamhuriyar Najeriya ta biyu Najeriya | ||||
Harshen uwa | Gbagyi | ||||
Ƴan uwa | |||||
Abokiyar zama | Fati Lami Abubakar | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Gbagyi Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da soja | ||||
Digiri | Janar | ||||
Imani | |||||
Addini | Musulunci | ||||
Jam'iyar siyasa | no value |
A lokacin mulkinshi ne Najeriya ta fidda sabon kundin tsarin mulki wato 1979 constitution, wanda ta bada daman zaɓe tsakanin jam'iyyu daban daban. Abdulsalam ya miƙa madakon iko ga sabon zaɓaɓɓen shugaba Olusegun Obasanjo a ranar 29 ga watan Mayu shekara ta alif ɗari tara da chasa'in da tara 1999. Shine Chairman na yanzu na National Peace Committee.[2]
Kuruciya
gyara sasheAn haifi Abdulsalam daga dangin Hausawa a ranar 13 ga watan Yuni shekara ta alif ɗari tara da arba'in da biyu 1942, mahaifinsa shine Abubakar Jibrin tare da mahaifiyarsa Fatikande Mohammed a Minna, Jihar Neja, Najeriya.
Abdulsalam ya halarci Minna Native Authority Primary school a tsakanin shekarar alif ɗari tara da hamsin 1950 zuwa shekarar alif ɗari tara da hamsin da shida 1956. A tsakanin shekara ta alif ɗari tara da hamsin da bakwai 1957 zuwa shekarar alif ɗari tara da sittin da biyu 1962 yayi karatunsa na sakandare a Government College, Bida, jihar Neja.
Aikin Soja
gyara sasheSojin Sama
gyara sasheAbdulsalam na cikin fitattun ɗaliban sojan sama da suka fara a ranar 3 ga watan Octoba shekara ta alif ɗari tara da sittin da uku 1963. A tsakanin shekara ta alif ɗari tara da sittin da huɗu 1964 zuwa shekarar alif ɗari tara da sittin da shida 1966, an ɗauke su zuwa garin Uetersen dake yammacin ƙasar Germany domin ƙara samun horo na musamman. A lokacin da suka dawo Najeriya a shekara ta alif ɗari tara da sittin da shida 1966, an mayar dashi zuwa sojin ƙasa.
Rayuwarsa a matsayin sojan kasa
gyara sasheBayan ya cigaba a matsayin sojan ƙasa a shekarar alif ɗari tara da sittin da shida 1966, Abubakar ya ziyarci Short service combatant two, inda ya fito a matsayin second lieutenant a watan October shekara ta alif ɗari tara da sittin da bakwai 1967, a sahib yaki. A tsakanin shekara ta alif ɗari tara da sittin da bakwai 1967 zuwa shekarar alif ɗari tara da sittin da takwas 1968 Abdulsalam Abubakar ya riƙe matsayin General Staff Officer two, Garrison officer sannan kuma Commanding officer, sannan kuma 92 infantry batallion a tsakanin shekarar alif ɗari tara da sittin da tara 1969 zuwa shekara ta alif ɗari tara da saba'in da huɗu 1974. A tsakanin shekarar alif ɗari tara da saba'in da huɗu 1974 zuwa shekarar alif ɗari tara da saba'in da biyar 1975 an bashi matsayin Brigade manjo bataliyar yaki na 7. A shekarar alif ɗari tara da saba'in da biyar 1975 yayi aiki a matsayin commanding officer, bataliyar yaƙi na 84. Har wayau, tsakanin shekara ta alif ɗari tara da saba'in da takwas 1978 zuwa shekarar alif ɗari tara da saba'in da tara 1979 Abdulsalam ya riƙe matsayin commanding officer na bataliyar yaƙi na 145 (NIBATT II), United Nations Interim force, dake ƙasar Lebanon.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Abubakar, Abdulsalam (2015). Financial development, impact on output and its determinants: the case of the economic community of the West African states. Kulliyyah of Economics and Management Sciences, International Islamic University Malaysia.
- ↑ "Buhari, Abdulsalami's national peace committee meet". Punch Newspapers. Retrieved 29 May 2020.