Jump to content

Usmar Ismail

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Usmar Ismail
Rayuwa
Haihuwa Bukittinggi (en) Fassara, 20 ga Maris, 1921
Ƙabila Minangkabau (en) Fassara
Mutuwa Indonesiya, 2 ga Janairu, 1971
Ƴan uwa
Mahaifi Ismail Dt. Manggung
Mahaifiya Siti Fatimah Zahra
Yara
Ahali Abu Hanifah (en) Fassara
Karatu
Harsuna Indonesian (en) Fassara
Sana'a
Sana'a darakta, mai tsara fim, maiwaƙe da marubin wasannin kwaykwayo
Employers PERFINI (en) Fassara
Kyaututtuka
IMDb nm0411344

Usmar Ismail (20 ga watan Maris shekara ta 1921 zuw 2 fa watan Janairu shekara ta 1971) ya kasance darektan fina-finai na kasar Indonesiya kuma marubuci, ɗan jarida kuma mai juyin juya hali na zuriyar Minangkabau . An dauke shi a matsayin dan asalin kasar Indonesiya na farko na fina-finai an kasar Indonesia.

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ismail a shekara ta 1921 a Bukittinggi, Yammacin Sumatra . Mahaifinsa, Datuk Tumenggung Ismail, ya koyar a makarantar likita a Padang . Ɗan'uwansa Abu Hanifah shi ma sanannen mai juyin juya hali ne kuma marubuci. Ismail ya halarci ASM-A Yogyakarta kuma daga baya ya samu kammala karatun B.A. a cikin fim a Jami'ar kasar California, Los Angeles a shekara ta 1952.

Ismail da farko ya yi aiki sojo a lokacin mulkin mallaka na Dutch. Ya yi aiki a cikin sojojin kasar Indonesiya a Yogyakarta . A wannan lokacin, ya kafa jaridar da ake kira Rakyat, ma'ana "people " or "populace " a cikin Bahasa Indonesia. Ya yi aiki a matsayin shugaban Kungiyar 'yan jarida ta kasar Indonesia a shekara ta 1946 zuwa shekara ta 1947. A kuma shekara ta 1948, an kama shi yayin da yake aiki a kamfanin dillancin labarai na kasa Antara don rufe tattaunawar Dutch-Indonesia.