Pele
Edson Arantes do Nascimento (lafazi|ˈɛtsõ (w)ɐˈɾɐ̃tʃiz du nɐsiˈmẽtu; an haifeshi ranar 23 ga watan Octobar, 1940- ya mutu ranar 29 ga watan Disamba 2022) anfi saninsa da Pelé (peˈlɛ) tsohon dan'wasan kwallon kafane na kasar Brazil, wanda yake buga gaba. Wadanda ke wasanni har da marubuta wasan ƙwallon ƙafa, yan wasa, da yan kallo (magoya bayan) na ganinsa a matsayin babban ɗan wasa a duniya. A shekara ta 1999, an zaɓe shi Dan Ƙwallon FIFA na ƙarni na Duniya daga hukumar International Federation of Football History & Statistics (IFFHS) kuma yana daga cikin biyun da aka zaɓa aka ba kyautar ɗan ƙwallon FIFA na ƙarni a wannan shekarar, an zabi Pelé amatsayin ɗan wasan motsa jiki na ƙarni daga hukumar International Olympic Committee. A cewar IFFHS, Pelé shine wanda yafi kowa samun nasarar zura kwallaye a raga a gasar league goal-scorer a tarihin kwallon kafa, inda ya zura kwallaye 650 a wasanni 694, League matches, a kuma gaba daya wasanni da yayi guda 1363 yaci kwallo 1281, har wasannin sada zumunci. Har wayau Pele shine Guinness World Record.[1][2][3][4][5] A lokacin da yake wasannin sa, Pelé shine wanda akafi biya acikin yan'wasa a duniya.
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 21 ga Disamba 2022, Asibitin Albert Einstein, inda ake jinyar Pelé, ya bayyana cewa ciwon kansar sa ya ci gaba kuma yana buƙatar "kulawar gaggawa game koda da zuciyarsa kan rashin aikin (dysfunctions) na ɓangarorin yanda ya kamata".[6] Pelé ya mutu a ranar 29 ga Disamba 2022, yana da shekaru 82 a duniya, sakamakon gazawar gabobi da yawa, mai rikitarwa na kansar hanji.[7][8]
'Yan wasan ƙwallo na duniya sun nuna alhininsu akan tsohon shahararren ɗan kwallon, ciki har da Neymar, Cristiano Ronaldo, Kylian Mbappé da Lionel Messi, da sauran manyan jiga-jigan ƴan wasanni, shahararrun mutane, da shugabannin duniya.[9][10][11][12] Shugaban Brazil, Jair Bolsonaro, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a ƙasar.[13] An ɗaga tutocin ƙasa na ƙungiyoyi 211 na FIFA a hedkwatar FIFA da ke Zürich.[14] Filayen wasannin an ɗaga tutoci don girmama Pelé cikin filayen da suka daga wannan tuta sun haɗa da; Christ the Redeemer da filin wasa na Maracanã Stadium a birnin Rio de Janeiro,[15] hedkwatar CONMEBOL a Paraguay[13] da filin wasa na Wembley Stadium a London.[16]
Za a yi jana'izar Pelé a filin wasa na Santos a ranakun 2 da 3 ga watan Janairu 2023.[17][18]
Binnewa
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan jana'izar, za a binne Pelé a Memorial Necrópole Ecumênica.[19]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ http://www.guinnessworldrecords.com/news/2013/10/video-pel%C3%A9-honoured-with-two-guinness-world-records-achievements-in-london-52558/
- ↑ http://pele.m-qp-m.us/english/pele_statistics.shtml
- ↑ http://www.rsssf.com/players/prolific.html#pele
- ↑ http://futdados.com/raio-x-dos-gols-de-pele-na-carreira/
- ↑ https://iffhs.de/?7e4a952bd814fc4d813e8a81be4ac0385fdcdc3bfcdc0aec70aeecf8a3c0d84411
- ↑ "Pele's cancer has advanced, says hospital". BBC Sport (in Turanci). Retrieved 21 December 2022.
- ↑ "Brazilian football legend Pele dies at age 82". www.aljazeera.com (in Turanci). Retrieved 30 December 2022.
- ↑ "Brazilian football icon Pele has died at the age of 82". Sky News. 29 December 2022. Retrieved 29 December 2022.
- ↑ "Pele: Neymar, Kylian Mbappe and Cristiano Ronaldo among those paying tribute". BBC. Retrieved 29 December 2022.
- ↑ "Pele dies - live updates: Pele's final message to the world as tributes pour in from sporting royalty". Sky News. Retrieved 30 December 2022.
- ↑ "'Your legacy will be eternal': sporting world pays tribute to Brazilian legend Pele". Reuters News. Retrieved 30 December 2022.
- ↑ Roberts, Jamie (30 December 2022). "Will Smith leads celebrity tributes as world mourns Pele after icon's death". mirror (in Turanci). Retrieved 30 December 2022.
- ↑ 13.0 13.1 "Brazil starts three days of mourning as country lights up in memory of Pelé". ITV News (in Turanci). 30 December 2022. Retrieved 30 December 2022.
- ↑ "FIFA's flags at half mast to honour Pele". Reuters. Retrieved 30 December 2022.
- ↑ Watson, Katy; Chatterjee, Phelan (30 December 2022). "'Thank you, King': Brazil lights up in honour of Pelé". BBC News (in Turanci). Retrieved 30 December 2022.
- ↑ "Wembley arch lit up in Brazil colours in tribute to Pele". The Independent. 2022-12-29. Retrieved 2022-12-30.
- ↑ "'Pelé is eternal!': Tributes pour in from soccer stars, world leaders". The Washington Post. Retrieved 30 December 2022.
- ↑ "Pele's funeral and burial to take place in hometown Santos". AP NEWS (in Turanci). 29 December 2022. Retrieved 30 December 2022.
- ↑ Pedroso, Camilo Rocha,George Ramsay,Tara John,Flora Charner,Rodrigo (29 December 2022). "Brazilian soccer legend Pelé dies at 82". CNN (in Turanci). Retrieved 30 December 2022.