OkadaBooks
Iri | yanar gizo |
---|
Okada Books Dandamali ne na self-publishing da kuma sayar da littattafai da ke kasar Najeriya,[1] [2] wanda Okechukwu Ofili ya kafa a shekarar 2013.[3] Google 's "Google for Start-up Accelerator" ne ya zaba a cikin shekarar 2017.[4] A cikin shekarar 2018, ta shirya gasar rubuce-rubuce tare da haɗin gwiwar Bankin Guaranty Trust mai suna " Dusty Manuscript ".[5]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Okechukwu Ofili ne ya kafa OkadaBooks a shekarar 2013.[6][7] Sunan ya haɗe ne da okada-motar haya da babur da aka saba amfani da ita don kewaya zirga-zirga a Najeriya da sauran ƙasashen yammacin Afirka-da littattafai. An fara dandalin ne a lokacin da wanda ya kafa ya kasance marubuci a BellaNaija da YNaija, kuma ya ji takaicin yadda shagunan sayar da litattafai ba sa biyan shi kudin litattafai da aka riga aka sayar. OkadaBooks yana ba da littattafai azaman zazzagewar wayar hannu. [8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Tolu Ogunlesi (6 October 2015). "A new chapter in Nigeria's literature". Financial Times.
- ↑ Philip Nwosu. "Digital economy in Nigeria driven by innovative platforms– John Obaro", The Sun Online, 6 November 2020.
- ↑ Otosirieze Obi-Young (31 August 2018). "African Writers Series' Classics Now Available for Affordable Downloads on OkadaBooks". Brittle Paper. Retrieved 30 October 2021.
- ↑ Yomi Kazeem (20 March 2018). "Google is making good on its promise to bet more on African startups and developers". Quartz.
- ↑ Jayne Augoye (9 February 2018). " 'Dusty Manuscript' contest for budding writers berths in Lagos". Premium Times .
- ↑ Laju Iren (23 November 2016). "Okada books: How one company is 'recycling' the publishing wheel". Vanguard Nigeria Newspaper
- ↑ "Okadabooks: Warum Nigeria kein Kindle braucht". Deutsche Welle (in German). 4 October 2017.
- ↑ Kole Omotoso (13 March 2019). "Okada Books comes to the rescue!!!". The Guardian .